Shugaba Buhari wadda ya kasance shugaban kungiyaar ECOWAS yayi jawabi ga shugabannin kasar China da na Afrikada kuma wakilan kasuwanci a taron.
Hausastyle.com ta tattaro wasu manyan abubuwa da shugaban kasar ya fadi a jawabinsa.
1. Dangantaka tsakanin China da ECOWAS
Shugaba Buhari yace akwai kyakwyawar alaka a tsakanin China da kasashen Afrika. Yace halartan taron da shugabanni da jihohin ECOWAS suka yi ya nuna cewa akwai alaka mai kyau tsakaninsu da China.
Ya kuma yi godiya ga Shugaba Xi Jinping akan alkawarin ginawa hukumar sakatariya da yayi.
2. Rawar ganin da ECOWAS take tawa a Afrika
Shugaban kasar ya kuma ce yankin ECOWAS sune keda kaso 30% na yawan mutane a yankin Afrika.
3. Inganta tattalin arziki
Shugaba Buhari ya kuma bayyana cewa mambobin kungiyar ECOWAS na aiki akan manufofin da tsare-tsare don inganta ci gaban kasashensu da habbaka tattalin arziki.
4. Zuba hannun jarin China a Afrika na Yamma
Shugaba Buhari a madadin mambobin kasashen ECOWAS ya yi godiya ga gwamnatin China kan ci gaba da zuba jari a yankin Afrika tare da kokarin gina makoma mai inganci.
5. Nemawa mutanen ECOWAS Visa
Shugaba Buhari ya kuma nemi alfarman visa ga mutanen yankin Afrika yan kasuwa da dalibai dake neman ziyartan China.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:


No comments:
Post a Comment