Hadimin shugaban kasar akan sabuwar hanyar sadarwa, Bashir Ahmad, shine ya bayyana wannan sabon rahoto a shafin sa na dandalin sada zumunta na Twitter.
Da isarsa, hukumomin kasar China sun shirya masa tarbo na musamman wanda ya hada da pareti tare da mutane da dama da suka hallarci filin saukan jiragen domin maraba da shugaba Buhari.
Duba hotunnan irin tarbar girmar da aka yiwa Buhari a kasar Sin
HausaStyle.com ta ruwaito shugaba Buhari zai kai wannan ziyarar ne don halartar taron majalisar koli na bakwai na hadin kan kasashen nahiyar Afirka da kasar China, FOCAC da zai gudana a babban brinin Beijing daga ranakun 3 zuwa 4 ga watan Satumba.
Duba hotunnan irin tarbar girmar da aka yiwa Buhari a kasar Sin
Shugaba Buhari ya samu rakiyar uwargidansa, Aisha zuwa Beijing inda anan ne za’a gabatar da taron a babban dakin taron Great Hall.
Har ila yau, wadanda suka raka shugaban kasa sun hada da Gwamna Mohammed Abubakar, Akinwumi Ambode, Mohammed Badaru, da Rochas Okorocha, sai kuma Sanatoci da suka hada da Abdullahi Adamu, George Akume, Godswill Akpabio, Aliyu Wammako, da Minisotoci guda 9.
Duba hotunnan irin tarbar girmar da aka yiwa Buhari a kasar Sin
Bayan bude wannan taro, shugaba Buhari zai gana da shugaban kasar China Xi Jin Ping da Firai ministan kasar Li Keqiang, inda zasu tattauna batutuwan da suka shafi hanyar samar da kudaden da za’a aiwatar da wasu manyan ayyuka a Najeriya, tare da tattaunawa akan hanyar kara dankon zumunci tsakaninsu.
Duba hotunnan irin tarbar girmar da aka yiwa Buhari a kasar Sin
Duba hotunnan irin tarbar girmar da aka yiwa Buhari a kasar Sin
Daga karshe Buhari zai yi amfanin da wannan damar ta haduwarsa da shugaba Xi Jin Ping don samun bayanai daga jami’an gwamnatin China game da matsayin ayyukan da suke yi a Najeriya, musamman aikin wutar lantarki da na titunan jirgin kasa.




