Author Aisha Jega
Buratai, wadda yayi Magana a Jaji wajen yaye runduna 55 na musamman yace “a rayuwa, dole mutun ya fuskanci wasu kalubale.”
Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta rahoto cewa a yan kwanakin da suka gabata, akwai rahoton labarai dake cewa yan ta’adda sun kai hari ga sojoji a yankin arewa maso gabas inda akayi ikirarin cewa an kashe wasu sojoji.
Sai dai rundunar sojin ta karyata harin da kuma cewar ta rasa jami’anta.
Buratai yaje Jaji netare da rakiyan babban hafsan sojin Afrika ta Kudu, Laftanar Janar Lindile Yam wadda ya kawo ziyara kasar.
A baya HausaStyle.com ta rahoto cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa babu wani yanki a kasar dake karkashin ikon yan ta’addan Boko Haram a yanzu.
Ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 2 ga watan Satumba, a Beijing, kasar China yayinda yake bayyana wasu nasarori da gwamnatinsa ta samu a lokacin da yake jawabi ga ‘yan Najeriya mazauna kasar.
Shugaban kasar ya danganta nasarorin ga ayyukan da hukumomin tsaro suka gudanar wajen yakar ta’addanci a yankin arewa maso gabashin kasar.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:


No comments:
Post a Comment