- Amurka ta rage yawan man da take saye daga Najeriya da kaso 62 cikin 100
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
- Wannan dai babban nakasu ne ga tattalin arzikin Najeriya
- Najeriya ta dogara kacokan kan danyen man fetur din ta
Adadin danyen bakin man da kasar Amurka ke saye daga kasar Najeriya da ke a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari a yanzu haka yayi kasa da ganga miliyan uku a duk wata adadin da bai taba kai hakan ba a duk 'yan kwanakin nan.
Amurka ta rage yawan man da take saye daga Najeriya da kaso 62 cikin 100
Wannan dai kamar yadda masana tattalin arzikin kasa suka yi fashin baki ba abu bane da zai haifarwa da kasar da mai ido musamman ma yanzu da tattalin arzikin kasar ke farfadowa.
HausaStyle.com ta samu cewa a baya dai anyi lokacin da kasar ta Amurka take sayen miliyoyin gangunan mai daga Najeriya wanda kuma hakan ya taimaki kasar sosai.

