Yadda direba ya ci amanar ubangidansa ya yi wa diyarsa fyade ta dau ciki
Rashin hakuri, kwadayi da cin amana ya jefa wani direba mai suna Mr. Friday cikin tashin hankali sakamakon cin amanar uban gidansa.
Mr Friday wanda ke daukan yayan ubangidansa zuwa makaranta dai ya yi amfani da karfi kuma ya yi wa wata diyar ubangidansa yar shekara 13 fyade sakamakon haka yarinyar ta dau ciki. Majiyarmu ta ce lamarin ya faru ne bayan wata rana direba
Mr. Friday ya zo domin ya dauki yaran zuwa makaranta, kasancewa an yarda da shi har ma yana shiga cikin gidansu, kuma bayan kasancewa direba, abokin mai gidan ne wanda babban Manaja ne a wani Kamfanin man fetur a Sapele na jihar Delta. Bayan Friday ya shiga gidan ne sai ya tarar yarinyar tana fitowa daga dakin wanka, gogan naka ya rude kuma fa ya rungumeta ya tausheta ya yi mata fyade. Bayan ya aikata wannan aikin ne daga bisani kuma ciki ya shiga bayan wani lokaci, sakamakon haka ne iyayen yarinyar suka kore shi daga aikinsa kuma suka mika shi ga yansanda domin ya fuskanci tuhuma.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
- Gwamnati (38)
- Kannywood (10)
- Kimiya Da Fasaha (1)
- Labarai (20)
- Laifi (11)
- Muslims/Addini/Addu'a (1)
- Sirrin Jikina (3)
- Soyayya (2)
No comments:
Post a Comment