Soyayya: Yadda wasu masoya suka kwashi 'yan kallo a jami'ar Bayero ta garin Kano (Bidiyo)

 saurayin a cikin wani irin salo na koyi da turawa, ya fiddo zobe daga aljihun sa inda ya kuma bukaci budurwa da ta mika hannun ta domin ya saka mata.

Sai dai budurwar wacce take a cikin shiga ta hausawa sanye da doguwar riga da kuma jan gyale ta fashe da kukan murna ne inda ta ma kasa hada ido da shi.

Lamarin dai ya auku ne a gaban tsangayar koyon ilimin lauya ne dake a jami'ar Bayero dake Kano kuma dalibai da dama sun shaida aukuwar lamarin.

Ga dai bidiyon nan:

https://web.facebook.com/pulsenigeriahausa/videos/1525611217543762/