Da duminsa: Shugaban PDP na Legas, Salvador ya koma APC

Cif Moshood Salvador, shugaban jam'iyyar PDP na jihar Legas da aka cire daga mukaminsa ya bayyana canja sheka zuwa APC a yau, Litinin.
Salvador ya dade yana fama da matsaninciyar adawa daga tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na kasa kuma dan asalin jihar Legas, Cif Bode George.
Salvador ya bayyana ficewar sa daga daga PDP a gidansa dake benen Salvador a cikin garin Legas.
Ko a jiya naij.com ta kawo maku labarin cewar wasu masu taimakawa gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, sun ja zugar mutane fiye da 5,000 zuwa jam'iyyar APC.
Shugaban PDP na Legas, Salvador ya koma APC
Masu taimaka gwamnan su biyu sun bayyana ficewar su daga jam'iyyar PDP ne ranar Asabar yayin kaddamar da takarar tsohon hukumar tattarar haraji a jihar Delta, Onowakpo Thomas, dake neman jam'iyyar APC ta tsayar da shi takarar majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Isoko.

Yayin kaddamar da takarar ne mataimakan gwamnan biyu; Lucky Arumare da Uyoyou Edhekpo, suka bayyana fitar su daga jam'iyyar PDP tare da magoya bayansu fiye da 5,000

No comments:

Post a Comment